Kamfanin dillancin labarab Iqna ya habarta cewa, a zantawa da Ustaz Taruti daya daga cikin manyan alkalan gasar kur’ani a mataki na kasa da kasa, ya sheda cewa Ustaz Ragib Mustafa Galwash ya kasance taruraro ga dukkanin bangarori na karatun kur’ani ba a kasar Masar ab kawai har ma a mataki na duniya baki daya.
Taruti ya ce rasuwar Ustaz Ragib Mustafa Galwash babban rashi ne ga dukkanin al’ummar kasar masar, haka nan kuma bababn rashi ne ga dukkanin makaranta kur’ani na duniya da ma duniyar musulmi baki daya, ya yi addu’ar Allah ya jikansa da rahma.
Ustaz Taruti ya ce labarin rasuwarsa ya girgiza al’ummar kasar masar, musamman ma dai makaranta alkur’ani mai tsarki, tare da bayyan hakan a matsayin bababn rashin da ba za a maye gurbinsa, sai fatan Allah ya gafarta asa ya kuma baiwa iyalansa da sauran danginsa da al’ummar musulmi hakurin rashinsa.
Ya ci gaba da cewa Ustaz Galwash yana daga cikin wadanda suka kirkiro salon a musammana wajen kira’a da ake amfani da shi a halin yanzu wanda ya hada dukaknin bagarorin na karatun kur’ani, musamman ma dai irin wanda Masar ta yi fice a kansa.
Haka nan kuma ya kara da cewa irin wannan salon shi ne shi ne salin Munshawi, wanda Galwash ya ci gaba da shi, kuma rasuwar ta sanya an samu babban gibi a wajen ci gaba da irin wannan salon a kwarewa wajen karatun kur’ani irin nasu.
Taruti y ace akwai daruruwan makaranta kur’ani da suke alfahari da kasancewarsu suna bin tafarkisa a wajen kira’a, wanda hakan abin alfahari ne ga musulmi domin daya daga cikin hanyoyin raya kur’ani da ya kirkiro za ta ci gaba da wanzuwa.