IQNA

Sarkin Morocco Ya Bayar Da Umarnin Yin Nazari A manhajar Karatu A Kasar

22:43 - February 07, 2016
Lambar Labari: 3480119
Banaren kasa da kasa, Sarki Muhammad na 6 na kasar Morocco ya bayar da umarnin yin nazari dangane da yanayin manhajar karatu a kasar a bangaren addinin muslunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ina cewa, a jiya Sarki Morocco Muhammad na shida ya bayar da umarni ga ma’aikatar ilimi ta kasar ka yin nazari dangane da yanayin manhajar karatu na addini a makarantun kasar.

An gudanar da zaman ne a birnin Uyun da nufin tattauna muhimman batutuwa da suka shafi tsarin manhajar karatu tun daga shekara ta 2015 har zuwa shekara ta 2030.

Babbar manufar sarkin dai ita ce yin dubi kan tsarin karatu ta fuskar addini a kasar, ta yadda za a kauce ma fadawa cikin matsaloli na saka tunanin tsatsauran ‘ra’ayin addini a cikin cukatan yara domin kauce ma fadawa cikin kungiyoyin yan ta’adda.

Ya ce dole ne tsarin koyar da addini a kasar ya zama ya yi daidai da hakikanin koyarwar ta addini, wadda ke kira zuwa ga zaman lafiya tare da sauran bangarori na al’umma, kamar yadda kuma dole ne a yi la’akari da yanayin al’adu na al’ummar kasar.

Sarkin na Morocco ya ce mu’amala a tsakanin yan kasa bai kamata ta zama ta bauta ba, domin kuwa kowane mutum yana yanci da hakki, kuma dole ne agirmama hakkinsa da yancinsa.

3473486

captcha