Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na kamfanin dillancin labaran Saudiyya cewa, sarkin kasar Salman bin Abdulaziz a cikin jawabinsa ya bayyana cewa, harami biyu da ke akwai kasar aminci ne gare al’ummar kasar baki daya, tare da yin ishara da ayyukan ta’addanci da suke mara ma bay aba, ya nuna cewa su ba su tare da yan ta’adda.
Haka nan kuma sarkin na Al Saud ya ce basu shiga cikin harkokin wasu kasashe, saboda haka kada wasu su shiga cikin harkokinsu na cikin gida, kamar yadda ya raya cewa suna kare musulunci ne da musulmi da kuma kasashen musulmi a dukkanin abin da aka ga suna aikatawa.
Sarkin an Al Saud ya kara da cewa, addinin muslunci addinin rahma ne, saboda haka duk mai tayar da hankalinsu wasu baya yin koyi da addini, akan haka suna kira ga dukaknin yan kasar da su san cewa shi ne sarkinsu kuma shi ne wanda tsaron kasarsu ya rataya akansa, shi ne mai hidima ga dukkanin haramomi masu daukaka, kamar yadda kuma shi ne kare su daga makiya.