
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bawwab Alarab cewa, sahyuniyawa mazauna matsugunnan yahudawa yan kaka gida, a tsawon kwanaki biyar a jere suna ci gaba da kai farmaki kan masallacin Aqsa mai alfarama.
Rahoton ya ce yahudawan suna kai wannan farmakin ne tare da cikakiyar kariya daga jami’an tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila a cikin kayan sarki.
Yahudawan suna kai farmakin ne a kan masallata tare da ci zarafinsu da kuma yin kamalan batunci a kan addinin muslnhci da muslmi, kamar yadda suke bata bangaye ta hanyar yin zanen batunci ga musulmi.
Masallata a cikin wannan masallaci dai sun jima suna rokon gwamnatocin kasashen larabawa da su taimaka su takawa yahudawan birki kan cin zarafin da suke yi musu, amma kamar suna yin kira ga matattu.
Harmtacciyar kasar Isra’ila dai tana son ta rarraba masallacin Qods mai alfarma ne tare da haramta ma musulmi hakkinsu.