IQNA

Mutanen Yankin Qatif Sun Gudanar Da Tarukar Arbaeen Na Sheikh Nimr

19:43 - February 12, 2016
Lambar Labari: 3480131
Bangaren kasa da kasa, mutanen yankin Qatif da ke gabashin Saudiyya sun gudanar da taruka cika kwanaki arbaeen na shahadar Sheikh Nimr.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar PressTV cewa, alummar yankin Qatif da ke sun gudanar da taruka cika kwanaki arbaeen na shahadar Sheikh Nimr adukkanin yankin.

Bayanin ya ci gaba da cewa an gudanar da wadannan taruka ne a dukaknin biranen ad suke gabashin kasar ta saudiyya, kamar yadda kuma aka gabatar da jawabai ga mahalarta taruka, tare da bayyana shehin malamin a matsayin gwarzo.

Mahukuntan kasar ta Saudiyya dai sun dauki matakin kashe Sheikh Nimr bayan da suka nuna tsorata matuka daga kamalansa, inda yake yin suka dangane da zalunci da danniyar da ake yi wa al’ummar gabashin kasar.

Mutanen Bahrain ba a barsu a bay aba wajen gudanar da irin wadannan taruka na tunawa da cikar kawanaki arbain na shahadar Sheikh Nimr, wanda mahukunatn Al Saud suka kashe saboda dalilai na siyasa da bangaranci.

Masu zanga-zangar a Bahrain sun yi ta rera take mutuwa a kan Al saud, tare da la’antar mumanan ayyukan da suka aikatawa na kisan yan adam musamman mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah a cikin kasar da ma wasu kasashen yanin gabas ta tsakiya.

Kamar yadda kuma aka kwalaye da kyallaye da suka dauke da hotuinan sheikh Nimr, da kuma kalamai na nuna goyon bayan gare shi, da shan alwashin ci gaba da bin tafarkinsa na kiyayya da zalunci da neman yanci.

3474935

captcha