IQNA

Gasar Kur’ani Mai Tsarki Ta Hardar Kur’ani mafi Girma A Iraki

19:46 - February 12, 2016
Lambar Labari: 3480132
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wata gasar hardar kur’ani mai tsarki mafi a kasar Iraki wadda ta kebanci dalibai dubu daya masu hardar kur’ani a Karbala.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na Hubbaren Hussaini cewa, an fara gudanar da wannan gasa ne tare da halartar dalibai kimanin 800 daga yankuna daban-daban na kasar Iraki da suka taru a birnin na karbala mai tsarki.

Bayanin ya ce dukaknin masu halartar gasar sun fito ne daga jahohi 8 na kasar da suka taru a birnin na Karbala.

An bude taron gasar ne a jiya, inda Sayyid Ali Adel mahardacin kur’ani mai tsarki dan kasar ta Iraki ya fara da budewa da karatun kur’ani mai tsarki, kafin daga bisani kuma Sayyid Mutada Jamaluddin daga hubbaren Hauusai ya gabatar da jawabi dangane da manufar taron, inda ya bayyana cewa babbar manufar ita ce koyon darussa daga kur’ani.

Sheikh Abu Ihsan Albasari shi ne shugaban kwamitin alkalan da za su gudanar da alkanaci a gasar, ya bayyana irin abubwan da gasar za ta mayar da hankali a kansu, inda ya yi bayani dalla dalla kan yadda za a gudanar da gasar tun daga mataki na farko, har zuwa mataki na karshe, da kuma yadda za a fitar da wadanda suka zo a matakan da ake bukata.

Wananns hiri na samar da mahardan kur’ani mai tsarki guda dubu daya yana daga cikin ayyukan bangaren kula da ayyukan kur’ani na Hubbaren Hussaini ya dauki nauyin gudsanarwa, wanda kuma wannan gasa na daya daga cikin bangarorin shirin.

Tun kafin lokacin bangaren bayar da horo na Hubbaren Imam Hussain (AS) ya gudanar da rangadi a jahohin kasar, domin samar da wadanda za su iya kasancewa acikin wannan shiri kamar yadda aka tsara shi.

Daga cikin ayyukan da za su rika gudanarwa har da gudanar da karatukan kur’ani a lokutan tarukan ziyarar Arbaeen da sauransu, tare da bude ajujuwa na karatu ga masu ziyara a lokutan tarukan addini a hubbaren mai tsarki.

3474947

captcha