
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-ahd cewa, masu goyon bayan gwagwarmayar muslucni ta Hizbullah sun shiga kamfe domin kalu balantar matakin kamfanin facebook, inda suka bukaci duk mai gwagwarmaya ya saka hoto daya na Sayyid Hassan Nasrullah a cikin shafin.
N fara gudanar da wannan kamfe ne tun jiya, bayan da kamfanin ya dauki mataki cire hotunan domin nuna adawa gare shi.
Ya zuwa yanzu dai an saka hotunan Sayyid Hassan nasrullah da dama a cikin shafukan facebook domin nuna cikaken goyon baya ga kungiyar da kuma gwagwarmayarta, domin kwato yancin al'umma daga makiya yan mamaya.