
Kamfanin dillancin labaran iqna ya
habrta cewa ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na parlmany.com cewa,
Muhammad Mukhtar Juma’a minister mai kula da harkokin addini a kasar Masar, ya
bude wasu wuraren hardar kure’ani mai tsarki guda 7 a lardin Deqahliyya na
zamani.
Y ace bababr manufar bude wadannan
wurare ita ce tabbatar da cewa yara masu koyon karatun kur’ani mai tsarki suna
yin hakan ne tare da sanin abin da kur’ani mai tsarki yake koyar da su,
maimakon yadda akasaba wasu sukan hardace kur’ani mai tsarki amma ba su abin
dayke koyar da su na daga darussa ba.
Muhammad Mukhtar Juma’a y ace za mu
yi amfani da wadannan wurare domin koyar da yara kur’ani da kuma tarbiyantar da
su a kansa.
Ministan harkokin addini na kasar
Masar ya ce za a yi amfani da wasu alluna na zamani wato tablet wajen koyar da
yara kur’ani, domin hakan zai taimaka matuka wajen sanya su rike abin da ake
koyar da su cikin sauri kuma su rike shi.
Muhammad Mukhtar Juma’a ya kara da
cewa, za a koyar da yara daga shekaru 4 zuwa 18 hakinanin koyarwar addini da
kur’ani, maimakon barinsu su samu gurbataccen tunani dangane da addini da shi
kansa kur’ani mai tsarki.
Daga karshe ya ce ma’aikatarsa tana
bayar da muhimmanci matuka a wannan fage, musamman ma ganin cewa yanzu haka
wasu daga cikindaliban sun fara samun abin da ake butata bisa wannan sabon
tsari.