IQNA

Ministan Addini Ya Bukaci;

Gabatar Da Wani Shirin Tarbiyantar Da Mahardata Kur'ani Dubu 100 A Tunisia

23:15 - February 14, 2016
Lambar Labari: 3480139
Bangaren kasa da kasa, Muhammad Khalil minista mai kula da harkokin addini a kasar Tunisia ya bukaci da fara gudanar da wani shiri na tarbiyantar da mahardata kur'ani dubu 100 a kasar a cikin shekaru uku masu zuwa.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tunisien.ir cewa, Muhammad Khalil minista mai kula da harkokin addini a kasar Tunisiaa lokacin ganawa da Muhammad Mashfar, shugaban kwamitin hardar kur'ani a kasar ya bukaci da fara gudanar da wani shiri na tarbiyantar da mahardata kur'ani dubu 100 a kasar a cikin shekaru uku a nan gaba.

Ya ce ma'aikatar kula da harkokin addini a kasar za ta samar da dukkanin abubuwan da ake bukata a cikin shekaru domin tababtar da cewa an aiwatar da wannan shiri.

Muhammad Khalil ya ce suna goyon bayan irin dukkanin matakan da kwamitin kula da harkokin harkokin hardar kur'ani a kasar, kuma za su ci gaba da taimakawa.

A lokacin ganawarsu da Muhammad Mushaffar shugaban kwamitin mahardata na kasar, ya tabbatar masa da cewa za su yi iyakcin kokarinsu kan wannan shiri, yayin da shi kuma ya koka kan matsalolin da ake fuskanta ta wannan fuska, musammama dai rashin kayan aiki da suka kama.

3475438
captcha