
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar al’adu ta Qafqaz cewa, an gudanar da taron ne tare da halartar manyan mutane da suka hada da malamai da kuma wasu daliban jami’a.
An fara gudanar da taron ne bayan bude wurin da karatun ayoyin kur’ani mai tsarki, wanda daya daga cikin makaranta kur’ani ya gabatar.
Daga cikin muhimamn abubuwan da aka bayyana, har cewa Sayyid (SA) ita ce gwazuwa ta hakika, wadda ta bayar da babban misali da ke koyar da darasi ga dukkanin yan adama da kuma musulmi, musamman mabiya tafarkin iyalan gidan manzo.
Bayan ga jawaban da aka gabatar kan rayuwarta da kuam darussan da rayuwarta mai albarka ke koyar da yan adam ta fuskar sadaukantarwa, da tsoron Allah da kuma dogaro gare da hakuri, an gudanar da addu’oi daban-daban, da suka hada da addu’ar Faraj, ta neman gaggauta bayyana Imam Hujja (AS)