
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Dastur cewa, Shuki Allam babban malami mai bayar da fatawa a kasar Masar ya ce kwamitin da kebincike kan fatawoyin kafirta musulmi ya gamno cewa yan daesh auna fassara wasu ayoyi ne domin ayyukan ta’addanci.
A lokacin da yake gabatar da wani shiri a talabijin na kasar Masar, Allam ya ce abin mamaki ne yadda yan ta’addan suke yin amfani da wasu daga cikin ayoyin kur’ani mai tsarki domin baiwa kansu hujja wajen gudanar da ayyukan ta’addanci.
Ya ce yanzu haka sun fara gudanar da bincike kan wadannan ayoyi 50 domin gano hakinanin musabbabin abin da yasa yan ta’adda suke amfani da su har suka bata kuma suke batar da wasu da su, domin daukar matakai na wayar da kai kan sashintafsirin aoyin kur’ani, maimakon salon da yan takfiriyya suke bi na juya ma’anar ayoyin na hakika.