IQNA

Iyalan Wadanda Suka Suka Rasa Rayukansu A Mina daga Mali Za Su Kai Kara

16:49 - February 17, 2016
Lambar Labari: 3480149
Bangaren kasa da kasa, lauyan wasu daga cikin iyalan wadanda suka rasa rayukansu a Mina a lokacin aikin hajjin bana ya bayyana cewa za su shigar da kara kan gwamnatin Saudiyya.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na The Associated Press cewa, wasu daga cikin iyalan wadanda suka rasa rayukansu a Mina a lokacin aikin hajjin bana daga kasar Mali za su shigar da kara kan gwamnatin Saudiyya kan wannan batu.

Marcel Chekaldi lauya wasu daga cikin wadanda suka rasa rayukansu a Mina a aikin bana ya bayyana a birnin Bamako na kasar Mali cewa, suna shirin shigar da kara kan wannan lamari.

N kasha mutane kimanin 320 daga cikin mahajjatan kasar Mali a lokacin gudanar da aikin hajjin bana.

Lauyan y ace za su shigar da karar ne sakamakon rashin wani bayani daga mahukuntan Saudiyya kan makomar mutanen da suka mutu, wanda hakan ke nuna rashin daukar lamarin da muhimmanci.

Kamfanin dilalncin labaran Associated Press ya ce mutanen suna cewa na maganar mutum 2426 suka rasu a Mina amma adadin ya wuce haka nesa ba kusa ba, yayin da kuma su mahukuntan saudiyya suke cewa mutane 769 kawai suka mutu a Mina.

3476389

captcha