IQNA

Mutanen Bahrain Sun Gudanar Da Jerin Gwanon Tunawa Da Yunkurin Juyinsu

19:46 - February 18, 2016
Lambar Labari: 3480151
Mutanen Bahrain Sun Gudanar Da Jerin Gwanon Tunawa Da Yunkurin Juyinsu
Bangaren kasa da kasa, dubban mutanen kasar Bahrain sun gudanar da gangami da jerin gwano domin tunawa da farmakin da jami’an tsaron kasar suka kai kansu a ranar wata alhamis shekaru biyar da suka gabata.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Alalm cewa, an gudanar da jerin gwanon ne a yankuna daban-daban na kasar, domin tunawa da ranar Alhamis ta fabrairun 2011, inda aka yi musu kisan kiyashi a dandalin Lu’alu’a a hannun jami’an tsaron kasar.

Masu gangamin sun yi ta rera taken cewa suna nan kan bakansu na neman sauyi a cikin harkokin siyasar kasar, inda suke bukatar suyi na dimukradiyya maimakon mulkin kama karya a kasar.

Mutane da dama ne suka yi shahada wasu kuma suka samu raunuka da suka hada da mata da kanan yara a kasar Bahrain, sakamakon matakan da mahukuntan kasar suke na ganin sun murkushe yunkurin al’ummar kasar, da ke neman a yi adalci a cikin lamarin mulki, da kuma neman hakkokinsu a matsayinsu na yan kasa.

3476655

captcha