
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Hubbaren Husaini cewa, shirin mai taken Sayyid Ruqayyah (SA) zai dauki tsawon kwanaki 10 ana gudanar da shi.
Sheikh Ali Almutairi shugaban bangaren yada lamurran addini a wannan cibiyar hubbare mai tsarki ya bayyana cewa, wanann shiri zai kunshi mata ne daga sassa daban-daban na kasar ta Iraki a karkashin shirin wannan cibiya.
Ya kara da cewa bisa la’akari da cewa lokacin gudanar da shirin takaitacce ne matuka, saboda haka za a koyar da wasu ilmomin na dsaban baya ga kur’ani, kamar fiqhum kyawawan dabiu, da kuma akidun muslunci.
Saru Mahdi shugaban bangaren shirin tarukan bayar da horo ga mata a wannan cibiya ya bayyana cewa, an tanaji wasu hanyoyi na musamman domin bayar da wannan horo cikin sauri, da hakan ya hada hanyoyi na zamani domin karatu da kuma kuma hardsa.
Wannan shiri na horo mai taken Sayyid Ruqayyah (SA) ana gudanar da shiri ne a wannan cibiya ta hanyar bayar da horo kan ilmomin da suka danganci kur’ani har wasu bangarorin na addini.