
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin tashar Press TV cewa, Amurka ta tabbatar da cewa jiragen yakin saman ta sun kai hari kan wani sansanin hora da 'yan ta'adan (IS) a kasar Libiya.
Harin wanda aka kai a wannan juma'a yayi sanadin mutuwar mutane sama da 40 kamar yadda mahukunatan kasar ta Libiya suma suka tabbatar.
Amurka dai na zaton cewa ta kashe wani babban kwamadan kungiyar (IS) mai suna Noureddine Chouchane dake da hannu a hare-haren ta'adanci biyu da aka kai bara a kasar Tunusiya.
Wani jami'in karamar hukumar birnin Sabrata inda aka kai harin ya shaidawa masu aiko da rahotanni cewa dukkan wadanda lamarin ya rusa dasu 'yan asalin kasar ta Tunusiya ne, wanda bisa ga dukkan alamu a cewar sa membobin kungiyar (IS) ne.
Trump: Amurka Sanadiyyar Bayyanar Daesh
Dan takarar shugabancin Amurka Donald Trump ya zargi Amurka da cewa itace sanadin bayyanar kungiyar ta’addancin ta Daesh a 2003.
Shafin yanar gizo na Alalam y ace,a jiya Trump ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar Amurka George W. Bush ne sanadin bayyana wannan kungiya ta ta’addanci, sakamakon harin da ya kai Irakia cikin wannan shekara.
Ya ci gaba da cerwa matukar dai ana son a kawo karshen wannan kungiya ta ta’addanci sai an bi kadun abubuwa da dama da suka faru tun daga lokacin domin gano hakikanin abin ya faru kan wannan batu.
Ya ce bai san mene dalilin shugar amurka cikin Iraki ba, domin har yanzu ba a gano makaman kare dangi ba, kuma babu ko daya daga cikin wadanda suka kai harin 11 ga watan Satumba da ya fito daga kasar Iraki.