
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alwafd cewa, cibiyar bayar da fatawar ta kasar Masar ta bayyana abin da wannan nashara ta yi da cewa, cin zarafi ne na dukkanin musulmin duniya baki daya.
Wannan nashara dai ta saka zanen wata mata da ta saka hijabin muslunci tana dauke da tutar kungiyar tarayyar turai, inda wasu mutane fararen fata suke cin zarafinta tare da nuna ta a matsayin wata yar ta’adda bare.
Abin da ake son a nuna a cikin wannan shi ne, mata musulmi zuwa suka yi turai, asalin yankin ban a musulmi ba ne, mabiya addinin muslunci yan ci rani ne a nahiyar turai.
Cibiyar ta ce babban manufar masu yin haka ba komai ba ne illa ci gaba da kara yada akidar nan ta kiyayya da musulmi da muslunci a cikin nahiyar, lamarin da ke nuni da cewa masu yin hakan ba san abin da duniya take ciki ba.
Bayanin ya kara da cewa ya zama wajibi a kan hkumomi na kasashen turai da su dauki dukkanin matakan da suka dace domin shiga kafar wando da mas aikata wannan mummunan laifi na nuna bangaranci a tsakanin al’umma.
Domin kuwa ana nuna ma muslmi banbanci da kiyayya ne saboda addininsu da akidarsu ta addini, wanda kuma dokokin wadannan kasashe sun huwace wa kowa ya yi addininsa da bin akidarsa daidai da yadda addinibnsa ya koyar da shi.
Kamar yadda kuma bayani ya yi ishara da cewa, masu adawa da musulunci sun jahilce shi da kuma koyarwarsa mai tsarki, domin kuwa addinin musulunci addini ne na zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsa da sauran addinai, kamar yadda tarihin muslunci ya tabbatar da hakan.