
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Jaza’iris cewa, taron kaddamar wannan tarjama ya samu halartar malami da masana da kuma limaman masallatai na garin Tiziwuzu.
Tarjamar kur’ani a cikin wannan harshen a Amazigi yana da matukar muhimmanci ga mutanen kasar Algeria, domin shi ne harshen kasa a hukumance a gefensa kuma larabaci.
An kaddamar da wannan tarjama ne tare da haklartar Said Buzizi malamin jami’a kuma masani kan harkokin kur’ani da tarjamarsa a cikin harsna daban-daban.
An dai fi yin amfani da wannan harshe a yankunan da kabilun larabawan kasar Algeriya suke, domin kuwa dadden harshe ne wanda ya jima tun kafin zuwan harshen larabaci a yankin baki daya.
Shi dai wannan harshen a Amazigi an fi yin fani da shi ne a cikin nahiyar Afirka musamman a kasar Algeriya, sai kuma wani bangaren na Morocco da Libya, sai kuma kasashen Tunisia da mali.
Abin tuni a nan dai shi ne,a lokutan baya ana yin tarjamar kur’ani a cikin wannan harshe daga kasar saudiyya, amma yanzu yan kasar ta Algeriya ne da kansu a cikin kasarsu suke gudanar da aikin tarjamar.