IQNA

Kwace kafin Kur’anai Masu Dauke Da Kura-Kurai A Tunisia

23:32 - February 20, 2016
Lambar Labari: 3480158
Bangaren kasa da kasa, an bayar da umarnin kwace kwafin kur’ani mai tsarki a kasar Tunsia, saboda kura-kuran da aka samu wajen bugunsa.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tunisien cewa, ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar ce ta bayar da umarni kwace wadannan kwafin kur’anan da aka buga bisa ruwayar Qalun a cikin shekara ta 2002, wanda madaba’natar darul-fikr Beirut ta buga.

A cikin bayanin ma’aktar an bayyana cewa, a halin yanzu babu kwafinsa acikin kasuwa ko kuma shagunan sayar da littafai, domin tuna cikin watan Yunin 2012 aka fara kwacewa, tare da yin kira ga jama’a da su tattara shi a duk inda suka gani.

Ma’aikatar kula da harkokin addinin a kasar Tunisia ta kirayi yan kasar baki daya, da cewa su bayar da hadin kai wajen ganin an kawo karshen yaduwar wannan kur’ani da aka buga da yake dauke da kura-kurai masu yawa, domin bariin wannan kur’ani yana yawo ya sba ma shari’a.

Daga karshe kuma bayanin ya babu laifi ma’aikatau da cibiyoyin addini da suke da littafai da kuma dakunan karatu su bincika dukkanin littafan da suke da su musamman ma kwafin kur’ani, domin tabbatar da cewa babu irinsa, idan kuma an samu ba tare da bata lokaci ba sai mika su ga wannan hukuma.

3476772

captcha