
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shfain sadarwa na yanar gizo na 3robanews.com Radiyo kur’an na kasar Masar ya bayar da rahoton rasuwar Ustaz Ahmad Muhamamd Amir, fitaccen makarancin kur’ani na kasar masar.
Sheikh Ahmad Muhammad Amir dai babban makarancin kur’ani mai tsarki a kasar Masar, ya rasu yana da shekaru 89 da haihuwa.
Wannan babban malami kuma makarancin kur’ani mai tsarki dan kasar Masar ya kasance daya daga cikin malaman da irinsa suka yi karanci a Masar ta fuskar karatun kur’ani da kuma iliminsa, inda ake kwatanta shi da malamai irin su Sheikh Muhammad Rif’at.
An Gudanar da Janazar Sheikh Ahmad Amir
Shafin sadarwa na yanar gizo na Veto a Masdar ya habarta cewa, Khalid Ahmad Amir dan mariyin ya bayyana cewa, an gudanar da janazarsa a masallacin Almajibi a garin Faqus da ke cikin lardin Sharkiyya, tare da halartar dubban malamai da kuma danginsa da almajiransa da sauran jama’ar gari.
Ya kuma kore wasu bayanai da ke cewa an rufe shi ne a garin Salihiyya wanda shi ne mahaifarsa.