
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habrta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na hespress.com cewa, kasuwar baje kolin da ake gudanarwa abirnin kazablanka na kasar Morocco karo na 22 ta samu karbuwa matuka daga sassa daban-daban na kasa da kasa.
Bayanin ya ci gaba da cewa, daya daga cikin madaba’antun da suka kawo littafai ta bayyana cewa, kur’ani mai tsarki shi ne ya fi samun masu saye fiye da dukaknin littafai da aka bajea wurin.
Kumail Hubbullah shugaban madaba’antar Afrika Sharq ya bayyana cewa, hakia wannan baje koli na wannan shekara yana da cikin irinsa da ska yi nasara matuka fiye da kowane lokaci.
Ya kara da cewa baya ga littafai na addini, sun kawo littafai a dukkanin bangarori na siyasa, zamantakewa, lidssafi, adabi, tarihi, da kuma wasu imomi na daban, da suka hada har da littafai na ilimin falsafa.
Kumail Hubbullah ya ce a baje kolin da ya gabata sun gabatr da littafai da dama, amma a wannan karon sun zo da wasu sabbin littafai ne wadanda suka burge da dama daga cikin masu halartar baje kolin.
Duk da cewa baje kolin littafan ya samu halartar mutane da damadaga koina, amma kuma tarukan da aka gabatar a cikin babban dakin taro da ke wurin, tare da halartar manyan marubuta daga kasashen da masana, bai samu halartar mutane yadda ya kamata ba.