IQNA

Mahukuntan Bahrain Sun Kori Malamin Addini Daga Kasar

23:47 - February 22, 2016
Lambar Labari: 3480167
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan kasar Bahrain sun kori Sheikh Muhammad Khijasteh daga kasar zuwa kasar Lebanon.

Kamfanin dillanicn labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Aran News cewa, duk da irin kiran da kungiyoyin kare hakkin bil adama da malamai suika yi mahukuntan kasar Bahrain sun kori Sheikh Muhammad Khijasteh daga kasar zuwa kasar Lebanon saboda dalilai na bangaranci da siyasa.

Shafin sadarwa na mir’at Bahrain ya habarta cewa, an kori sheikh Muhammad Khojaste ne zuwa nirnin Beirut na kasar Lebanon.

Bayanin ya ci gaba da cewa, bayan korar sheikh Muhammad Khajaste, al’ummar kasar Bahrain sun nuna rashin amincewarsu da wannan bakin zalunci.

Tun bayan da al’ummar kasar Bahrain suka fara neman sauyi na siyasa ta hanyar luimana a cikin yan shekarun da suka gabata, mahukuntan mulkin mulukuyya na kasar sun dauki matakan azabtarwa da murkushewa kan al’ummar kasar, wadanda suke neman hakkokinsu da aka haramta musu a matsayinsu nay an kasa.

Malaman addini a kasar ta Bahrain sun fitar da bayanai da ke yin Allawadai da wannan mataki na zalunci da danniya da kuma kama karya kan farraen hula marassa kariya, inda suka kirayi mahukunan kasar da su janye wannan hukunci na korar sheikh Khojaste daga kasarsa ta haihuwa.

Tun daga lokacin da aka fara yunkurin neman yanci a kasar Bahrain a cikin yan shekarun nan, an kori mutane yan kasa daga zuwa wasu kasashen ketar inda ak atilasta musu yin gudun hijira, wadanda adadinsu ya kai 250m da ska hada da malaman addini 13 daga cikinsu.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama na ciki da wajen sun yi Allawadai da kakkausar murya kan wannan mataki na zalunci da mahukntan mulkin mulukiya na Bahrtain suka dauka kan wannan shehin malami, inda suka raba shi da kasarsa suka tilasta masa yin gudun hijira.

3477507

captcha