
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na wasu jaridun saudiyya cewa, mahukuntan kasar sun kame mutane 32 da ska hada da yan shi’a 30 bisa tuhumar cewa suna yi wa Iran liken asiri.
An dai kame mutanen ne tun a cikin shekara ta 2013, kuma aka ci gaba da tsare sub a tare da wani laifi ba, illa wannan tuhuma ta siyasa da take da alaka kai tsaye da batun akida, domin kuwa dukakninsu mutane da ba su da wata alaka da abin da ake zarginsu, kamar yadda kungiyoyin kare hakkin bil adama suka tabbatar.
Wannan dai bas hi karon farko da mahukuntan masarautar iyalan gidan saud suke daukar irin wanann mataki kan mabiya mazhabar shi’a ba, inda takan fake da wasu dalilai marassa kan gado domin kawai ta cutar da su.
A kwanakin baya baya masarautar mulkin kama karya ta Al saud ta kashe Sheikh Nimr daya daga cikin fitattun malaman shi’a a kasar saboda dalilai na bangaranci da zalunci.