
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa , a zantawarsa da Mohamad Reza Ghazall Sofli karamin jakadan kasar Iran Saliyo ya bayyana cewa, sakamakon rashin lafiya mai tsanani an dauke shi zuwa birnin Free Town fadar mulkin kasar domin yi masa magani a asibiti, amma bayanb dan lokaci ya rasu.
Ya kara da cewa Ibrahim Suri Sise ya kasance mutum ne mai kokari matuka wajen gudanar da shirin radiyo kan harkokin addini musamman ma a bangaren kur’ani da ilmominsa.
Ghazal Sofli ya kara da cewa an gudanar da janazarsa marigayi Ibrahim Suri a birnin an Free Town, kuma an bizne shia makabartar Gingdam da ke birnin.
Ya ci gaba da cewa marigayi Sise ya kasance yana rubuta makaloli a jaridun kasar Saliyo, inda yake yin bayani kan addini da kuma fallasa makircin wahabiya masu gurbata addinin muslunci, kuma fahimci mazhabar Ahll bait (AS)a kimanin shekaru 10 da suka gabata.