IQNA

An Fara Gudanar Da Gasar Kur’ani Mai Tsarki Ta Azhar

22:40 - February 24, 2016
Lambar Labari: 3480172
Bangaren kasa da kasa, Ana ci gaba da gudanar da gasar hardar kur’ani mai tsarki ta ‘yan kasashen ketare masu karatu a jami’ar Azahar da ke birnin Alkahira.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Misri Al-yaum cewa, bangaren da ke kula da harkokin gasar kur’ani da kuma cibiyar harkokin kur’ani mai zaman kanta a Najeriya su ne suka shirya gasar.

Bayanin ya ci gaba da cewa mahardata kur’ani 81 daga kasashe daban-daban suke gudanar da wanann gasa, inda ake tabo dukkanin bangarori kama daga hardar dukkanin kur’ani da kuma hardar juzu’I 15.

Usama Yasin shugaban bangaren kula da harkokin kur’ani na jami’ar Azhar ya bayyana cewa, ko shakka babu wannan gasa tana da matukar tasiri a dukkanin harkokin da ake gudanarwa da suka shafi kur’ania wannan jami’a.

Ya kara da cewa babbar manufar gudanar da gasar dai ita ce karfafa gwaiwar dalibai wajen mayar da hankali ga lamarin kur’ani mai tsarki, musamman ma wadanda suke karatu a bangaren ilmomin kur’ani a wannan jami’a.

Ya ce a halin yanzu gasar ta yi nisa atsakanin dalibai 81 da suke karawa da juna, inda za a ci gaba da zaftarewa har sai an kai ga matakin kusa da na karshe, daga nan kuma sai matakin da daga shi sai na karshe, sa’anan a gudanar da zaman karshe inda za a fitar da na daya.

Za a bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka nuna kwazo a dukaknin bangarorin da aka gudanar da gasar.

3478063

captcha