IQNA

Mai Fatawa A Saudiyya: Wahabiyanci Ya Tserar Da Mu

22:43 - February 24, 2016
Lambar Labari: 3480173
Bangaren kasa da kasa, wani daya daga cikin giggan malaman wahabiyawan Saudiyya ya gargadi yan kasar da cewa inda ba domin wahabiyanci da sun zama labara.

Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alalam cewa, Saleh Fauzan daya daga cikin giggan malaman wahabiyawa kuma mamba akwamitin bayar da fatawoyi na gwmnatin Saudiyya ya bayyana cewa, abin da Muhammad Bin Abdulwahab ya yi shi ne ya tseratar da su.

Fauzan ya ci gaba da cewa koyarwar da suka samu daga makarantar bin Abdulwahab ita ce ta sanya su suka kai matsayin da suke a yau, kuma ake dama wa da su, domin da ba don haka da tuni sun zama tarihi.

Haka nan kuma dangane da tsarin koyar da dalibai a makarantun kasar ya kara jaddada cewa, dole ne amayar da hankali wajen tabbatar da cewa wannan tsari na mahagar wahabiyanci ya ci gaba da tabbata, kuma ana aiki da shi a dukkanin makarantun kasar.

Gwamnatin kasar saudiyya wadda ta ginu kan akidar wahabiyanci kamar yadda kasar Birtaniya ta kafata tun bayan rusa daular turkawa da ta mulki kasar, ta daukar ma kanta yada wannan akida a dukkanin fadin duniya tare da taimakon turawan Birtaniya, matsayin wannan shi ne muslunci ko kuma sunnar annabi mai tsira da amincin Allah.

Akidar wahabiyanci dai it ace akidar kafirta sauran muslmi har da yan sunna da basu amince da ita ba, kamar yadda kumaita ce tushen dukaknin ayyukan ta’addancin da suka addabi duniya a halin yanzu.

3478087

captcha