
Kamfanin dillanicn labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ciiyar yada al’adu ta kasar Iran cewa, an fara share fage na taron karawa juna sani a Senegal, tare da fara gabatar da jawabai ga mahalarta, wanda kuma zai ci gaba har tsawon kwanaki biyu.
Bayanin ya ce bababr manufar gudanar da wannan taro dai ita ce kara wayar da kan musulmi kan muhimamncin fahimtar koyarwar kur’ani mai tsarki da kuma yin aiki da ita a cikin dukkanin lamurran rayuwa.
Kamar yadda kuma wadanda za su gabatar da jawabi za su tabo muhimman batutuwa da suka shafi gurbata fassarar kur’ani da wasu amsu dauke da mummunar akida suka yi, wanda hakan ne yake haifar da kungiyoyin yan ta’adda da sunan addaini.
Taron dai shi ne irinsa n farko da aka fara gudanarwa, wanda ya samu karbuwa matuka daga dukkanin bangarori na al’ummar musulmi mazauna wannan kasa, wadda take a yammacin nahiyar wannan nahiya.
Sayyid Hassan Ismati karamin jakadan kasar Iran a Senegal shi ne ya shirya wannan taro, wanda kuma wasu daga cikin malamai na kasar da kuma masana za su gabatar da makaloli.
Daga karshe masu shirya taron sun tabbatar da cewa an samu amsa gayyatar da aka akike zuwa ga malamai da dama musamman ma na jami’a masu gudanar da bincke kan lamurra na addini.