IQNA

Shugaban Kasa:

Zabe Wata Alama Ce Ta ‘Yancin Siyasar Kasa

22:42 - February 26, 2016
Lambar Labari: 3480179
Bangare siyasa, Dr. Hassan Rauhani ya bayyana cewa gudanar da zabuka wata babbar alama ce da ke nuna cewa kasa tana kan sahihin tafarki na ‘yancin siyasa a mahanga ta muslunci.

Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta cewa, Shugaban kasar Iran ya bayyana cewar gudanar da zabuka a kasa wata babbar alama ce da ke gwada 'yancin siyasa da shugabanci a kasa.

A taron manema labarai da ya gudanar a bayan kada kuri'arsa a zabukan 'yan Majalisun Dokoki da na Majalisar kwararru masu zaben Jagoran juyin juya hali a Jamhuriyar Musulunci ta Iran a yau Juma'a: Shugaban kasar Iran Sheikh Hasan Ruhani ya jaddada cewa; Tabbas yana daukan kuri'ar al'umma a matsayin wata babbar amana, don haka ya zame dole kowa ya yi iyaka kokarinsa a fagen kare wannan amana da al'umma ta dora masa.

Sheikh Hasan Ruhani ya kara da cewa; Kafin samun nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran 'yan mulkin mallaka ne suka juya akalar kasar, amma a halin yanzu al'ummar Iran ne ke rike da ragamar Iran kuma ta hanyar gudanar da zabe ne al'ummar Iran zasu kasance sun ci gaba da jagorantar kasarsu cikin yanci.

Ya ci gaba da cewa ya zama kan al’ummar kasar Iran baki daya su kwana da sanin cewa, ra’ayoyinsu kowane su ne suke fayace makomar kasar a bisa tafarkin dimukradiyyar muslunci wadda kasar take tafiya a kansa.

Dangane da iyadda wasu kasashe masu fatan ganin abin sharri ya sami kasar kuwa, Rauhani ya jadda cewa a kowane lokaci su suna fatan alkhairi ne ga kowa, kuma basu nufin kowane da mummuna koda kuwa shi ya nufe su da hakan.

Haka nan kuma ya jadda cewa za a ci gaba da bin wannan salon a kiyaye hakkokin al’umma da ra’ayoyinsu a cikin dukkanin lamurra da suka shafi kasar da kuma makomarta.http://iqna.ir/fa/news/3478374

Daga karshe ya yi kira ga daukacin mutanen kasar Iran da su ci gaba da bayar da himma a cikin dukkanin bangarori kamar yadda aka sansu, domin hakan shi ne yancinsu shi ne kuma ya basu daukaka, maimakon tsayawa wajen dogaro da wasu, wanda suke dora siyasarsu kan al’ummomi.

Kamar yadda kuma ya ja hankalin dukaknin yan takara da su zama masu cika alkawullan da suka Dakar wa al’umma kasar, domin kuwa babban abin da mutane za s fara sanya ido a kansa bayan sanar da sakamako da kuma kama aiki, shi ne alkawullan da aka yi musu, domin ganin shin an cika su ko kuwa sabanin hakan.

3478374

captcha