IQNA

Za A Gudanar Da Gasar Kur’ani Mai Tsarki Ta Ajman A UAE

22:45 - February 26, 2016
Lambar Labari: 3480181
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki da sunnar manzo ta AJMAN wadda cibiyar Darul Bar take daukar nauyin gasar.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na KTimes cewa, kimanin daliban makarantun sakandare 1500 ne za su halarci wannan gasa, da suka hada da mata da kuma maza.

Wadanda suke da bukatar shiga cikin gasar dai suna da lokacin yin rijista daga nan har zuwa mako guda mai zuwa kafin a rufe rijistar baki daya.

Babbar manufar gudanar da wannan gasa dai ita ce tabbatar da cewa an bayar da haske na kara sanin kur’ani mai tsarki da kuma sunnar manzon Allah (SAW)

Ana bayyana cewa hardar kur’ani mai tsarki tana da babban tarihin ga yaro, a kan haka aka fara gudanar da wannans hiri na harda ga yara yan makaranta tun daga shekara ta 2011 da ta gabata.

3478324

captcha