
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na World Bulletin cewa, palastinawa 29 ne suka yi shahada a lokacin da yahudawan Isra’ila suka bude wuta kansu a ranar 25 ga watan Fabrairun 1994 a garin Khalil.
Bayanin ya ci gaba da cewa, a daidai lokacin da ake gudanar da wannan gangami jami’an tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi amfani da hayaki mai sanya hawaye wajen tarwatsa su.
Haka nan kuma sun hana wasu da dama isa wurin da ake gudanar da wannan gangami, inda suka tilasta su koma, yayin da kuma wadanda suke wurin suka tarwatse.
Rahotanni sun ce an kame daya daga cikin masu zanga-zangar kuma an yi wani wuri da shi da ba a sani ba.
Tun a cikin shekarar da ta gabata ce dai aka fara gudanar da boren quds inda yazuwa yanzua cikin yan watanni da suka gabata an kash epalastinawa 190 da suka yi shahada.
Babban abin ban mamaki dais hi ne yadda kasashne duniya suka gum da bakunansu kan wannan ta’addanci da yahudawan sahyuniya suke yi kan palastinawa.