IQNA

An Bude Cibiyar Kur’ani Ta Rasul A’zam (SAW) A Birnin Bagadaza

23:47 - February 27, 2016
Lambar Labari: 3480184
Bangaren kasa da kasa, an bude cibiyar karatun kur’ani da kum akoyon ilmiminsa ta Rasul A’azam (SAW) a arewacin birnin Bagadaza tare da halartar malamai da kuma makaranta.

Kamfanin dillanicn labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na QAF cewa, a yayin gudanar da taron bude wannan cibiya ta Rasul A’azam (SAW) an gudanar da jawabai a masallacin Rasul A’azam (SAW) da ke ynakin Al-sha’ab da ke arewacin birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki.

Tashar talabijin ta Almasar Al’ula ce ta dauki nauyin watsa shirin kai tsaye a lokacin gudanar da shi.

Wadanda za su dauki nauyin kula da sanya ido kan dukkanin harkokin wannan cibiya dais u ne Sayyid Majid Mubarqa babban limamin masallacin Rasul A’azam (SAW) da kuma Sheikh Iyad Alka’abi, daya daga cikin fitattun makaranta kur’ani na kasar.

A yayin gudanar da taron bude wannan babbar cibiya ta kur’ani mai tsarki an samu halartar fitattun malaman kur’ani da makaranta, da suka hada da Sheikh Rafe Ala’miri, Sheikh Iyad Alka’abi, Sheikh Usama Karbala’I, Ali Muhammadawi da dai sauransu.

3478747

captcha