IQNA

Malaman Musulmi Sun Yi Allawadai Da Barazanar Kai Hari Kan masallatai A Holland

16:44 - February 29, 2016
Lambar Labari: 3480190
Malaman Musulmi Sun Yi Allawadai Da Barazanar Kai Hari Kan masallatai A Holland
Bangaren kasa da kasa, kwamitin malaman addinin musulunci yan kasar Morocco CEOM mazauna nahiyar turai sun yi Allawadai da barazanar kai hari kan masallatai a cikin kasar Holland.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, kwamitin malaman muslunci mabiya tafarkin sun yan kasar Morocco mazauna nahiyar turai sun bayyana cewa, wannan cin zarafi ne ga dukaknin mabiya addinin musulunci.

A cikin wani bayani da suka fitar sun bayyana cewa, wadanda suke yin wanann barazana mutane ne marassa son zaman lafiya, kuma suna yin amfani da akidarsu ta kin muslunci wajen aiwatar da manufofinsu.

Daga cikin irin abubuwan da suke yi kuwa har da saka alamomi na muzunta muslunci ta hanyar keta alfarmar masallatai inda sukan saka hotunan sakandami ko kuma alarm jam’iyyar nazy a kan bangayen masallatan.

Kamar yadda kuma a cikin kwanakin suna rubuta wasu wasiku suna rabawa ga cibiyoyin muslunci da masallatai da musulmi suke taruwa suna gudanar da harkokin addini, suna barazanar cewa za su kawo hare-hare a wadannan wurare.

Baya ga hakan kuma an samu daga cikinsu da suke cin zarafin musulni ta hanayar zaginsu da yi musu izgili a kan hanya ko a sauraren wurare na taruwar jama’a a cikin kasar ko kuma a sauran wurare na aiki.

A kan haka bayanin ya ce dole ne a dauki dukaknin matakan da suka dace domin shawo kan wannan matsala wadda ta zama babbar abin bakin ciki ga al’ummomin musulmi mazauna wadannan kasashe.

Abin tuni a nan shi ne a ranar Alhamis da ta gabata ce wasu masu gaba da addinin muslunci a kasar ta Holland suka yi barazanar kai hari kan wani masallaci na mabiya addinin muslunci a kasar.

3479278

captcha