
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gioz na wishtv cewa, a jiya a wani mataki na kin addinin muslunci da wasu Amurkawa suke nunawa musulmi, sun kai hari kan ginin babbar cibiyar muslunci a arewacin kasar Amurka.
July Nast wata makwabciyar wurin da abin ya faru ta bayyana cewa, haki wannan babban abin bakin ciki ne ya faru.
Jim kadan bayan faruwar lamarin cibiyar ta buga wa jami’an yan sanda na FBI domin su kawo musu dauki
Tun a cikin shekara ta 1982 wannan cibiya take gudanar da ayyukanta addini ba tare da wani tashin hankali ba.
Nast ta ce ba mu cika ganin irin wannan abu ba musaman a kan wanann cibiya wadda ta jima tana gudanar da harkokinta cikin hanyoyi na zaman lafiya.
Cibiyar NASA ita ce cibiyar musulmi mafi girma kuma mafi dadewa a kasar Amurka baki daya.
Jami’an yan sanda sun zo wurin kuma sun dauki hotuna a daidai wurin da abin ya faru, amma har yanzu ba su uffan kana bin da ya faru ba, kamar yadda kuma ba su sanar da sakamakon bincike ba.
Daga karshe dai wanann baa bin mamaiki ba ne kuma bas shi ne karo na farko da aka kai hari kan wata cibiyar mabiya addinin muslubci a kasar Amurka ba, domin kuwa an yi hakan da dama.