
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Alalam cewa, Tayyib ya bayyana cewa babban abin muni yadda musullmi suka zama suna riki saboda banbancin mazhaba.
Babban malamin jami'ar Azhar ta kasar Masar ya jaddada cewa; Haramtacciyar kasar Isra'ila ce kadai ke amfana daga duk wani rikicin mazhaba da ke faruwa a tsakanin al'ummar musulmin duniya musamman a yankin gabas ta tsakiya.
A jawabin da ya gabatar a jiya Litinin shugaban babban jami'ar Azhar da ake kira da Sheikhi Azhar Ahmad Tayyib ya jaddada cewa; Tashe-tashen hankulan da suke faruwa a sassa daban daban na duniya da sunan addinin Musulunci musamman rikice-rikicen mazhaba a yankin gabas ta tsakiya al'amura ne da suke amfanar da makiya addinin Musulunci musamman yahudawan sahayoniyya da suka kafa haramtacciyar kasar Isra'ila.
Sheikh Ahmad Tayyib ya kara da cewa: Kungiyoyin Musulunci sune kan gaba wajen raba kan al'ummar musulmin duniya, don haka ya zame dole a kan kasashen musulmi su fadaka domin fuskantar babban hatsarin da ke fuskantar al'ummar musulmin duniya musamman ayyukan ta'addanci da sunan addinin Islama.
A cikin wannan shekara dai kasar Saudiyya tana da shirin gina makarantu kimanin dubu 24 a cikin kasar Pakistan, da nufin yada mummunar akidar nan ta wahabiyanci wadda ke haifar da tunanin ta’addanci da sunan addinin a cikin kasashen musulmi, lamarin da masana a kasar ta Pakistan ke kallonsa a matsayin wani babban hadari.