IQNA

Gasar Karatun Kur’ani Da Tajwidi A kasar Mauritaniya

15:28 - March 01, 2016
Lambar Labari: 3480194
Bangaren kasa da kasa, za a fara fara gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki da kuma tajwidi a kasar mauyritaniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sahara Media cewa, babban cibiyar hardar kur’ani ta kasar Mauritaniya ta sanar da cewa wadanda suke da bukatar yin rijista suna ita buga waya tarho 36117333-38280000 a kowane lokaci.

Bayanin ya ci gaba da cewa za a gudanar da wannan gasa ne karkashin shirin na gasar Nur a birnin Nuwakshot fadar mulkin kasar, wadda aka saba gudanarwa a kowace shekara.

Haka nan kuma ya kara da cewa ya zuwa yanzu an samu wadanda suka yi rijistar shiga wannan gasa mai matukar farin jinni a tsakanin al’ummar kasar.

A duk lokacin da ake gudanar da wannan gasa akan samu kafofin yada labaran wadanda suke watsa ta kai tsaye, da hakan ya hada da gidajen radiyo da kuma talabijin.

Babban masallacin Ridhwan da ke birnin Nueakshout kan dauki nauyin gudanar da wannan gasa, duk kuwa da cewa babban cibiyar kula da ayyukan kur’ani da shiya gasa tana yin hadin gwiwa da kwmitin masallacin.

Bayan kammala gudanar da gasar dai ana bayar da kyautuka na musamman ga wadanda suka nuna kwazoa dukkanin bangarori na gasar a kowace shekara, daga nan kuma sai rufe taron.

3479673


captcha