IQNA

An Fara Gdanar da Wani Kamfe Na Haramta Wahabiyanci A Amurka

23:42 - March 02, 2016
Lambar Labari: 3480196
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani kamfe na haramta wahabiyanci a kasar Amurka wanda babbar cibiyar musulmin kasar gami da wasu kungiyoyin kiristoci suka fara yi tare.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin yanar gizo na Aran News cewa, wannan kamfe an fara shi ne a wasu daga ciki manyan birnan kasar, domin fadakar da mutane su gane babban hadarin da yake tattare da wannan akida ta wahabiyanci.

An fara kamfen din ne a kan tituna ta hanyar raba makaloli da bayanai da aka rubuta ga masu wucewa, domin su zama suna da masaniya kan hakikanin abin da ake kira akidar wahabiyanci da kuma banbancinta da akidara ddinin muslunci.

Wasu daga cikin kiristoci ana bayyana musu hakinain wannan akida ne saboda kuren da suke yi wajen daukar dukaknin masu wannana kida wadda take haifar da ta’addanci da duniya take ganin a halin yanzu a matsayin hakan shi ne addinin muslunci.

Wanda kuma ko shakka babu hakan ne yasa suke kallon musulmi a matsayin ‘yan ta’adda ko kuma addinin muslunci a matsayin addinin ta’addanci saboda rashin sanin banbanci tsakanin muslunci da kuma wahabiyanci.

Yayin da su kuma msuulmi ake jan hankalinsu domin kwa su ne suka fi fdawa cikin wannan tarkon wannan mummunar akida wadda gwamnatin kasar saudiyya ce da kanta take yada ta a duniya, kuma ta hakan ne ake samar da gingan yan ta’adda wadanda tantagaryar jahilai ne bas u san komai kan addinin muslunci ba, a matsayin masu jihadi.

Masallatan da wahabiya suke ginawa a kasar Amurka sun zama wurae na yada tsattasaraun ra’ayi, wanda kuma daga nan sai shiga ta’addanci, wanda kuma hakan yana tattare da hadarori masu muni, a kan haka kiristoci da ska gane hakan tare da sauran musulmi suka dauki wannan mataki domin kada a bata sunan muslunci.

3480130

captcha