
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Alalam cewa, mutanen kasar Bahrain na gudanar da wani gagarumin jerin gwano a dukaknin fadin kasar domin tunawa da zagayowar lokacin mamaye kasarsu da Saudiyya ta yi wanda ya cika shekaru biyar.
Babbar manufar wannan jerin gwano dais hi ne tunawa da zagayowar wanann lokaci na shigowar yan mamaya a cikin kasarsu, da kuma neman ficewarsu.
Tun bayan da aka fara yunkurin neman sauyi na dmokradiyya akasar Bahrain mahukuntan kasar tare da hadin baki da mahukuntan saudiyya dama wasu yan koranta na yankin kamar su hadaddiyar daular larabawa, sun kaddamar da farmaki da dukaknin karfinsu akna l’ummar Bahrain..
Manufar kai wannan hari da farmaki da yin kisan gilla kan mata da kanan yara da tsoffi, ita ce murkuhs eyunkurin al’ummar kasar, wanda in har yay i nasar to ya bayar da dama ga sauran al’ummomin larabawa da sarakuna suka danne domin su motsa su samu yanci.
A ranar 14 ga watan Fabrairun shekara ta 2011 ne daia mutanen Bahrain suka fito kwansi da kwarkwatarsu domin nuna rashin yarda salon mulkin zalunci da Danni na muluiya na masarautar kasar, wadda kasashen turai ke marama baya, tare da taimaka mata da makamai domin kahe yan kasar.