IQNA

Hizbullah: Kudirin Sarakunan Larabawa Kan Kungiyar Tsabar Jahilci Ne

22:45 - March 04, 2016
Lambar Labari: 3480201
Bangaren kasa da kasa, yan majalisar dokokin kasar Lebanon daga bangaren kungiyar Hizbullah, sun bayyana kudirin larabawan yakin tekun fasah da cewa aiki ne na jahilci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar Alalam cewa, yan majalisar dokokin kasar Lebanon daga bangaren kungiyar Hizbullah, sun bayyana matakin da sarakunan larabawan yankin tekun farisa suka dauka na saka kungiyar cikin kungiyoyin 'yan ta'adda da cewa ba a bin mamaki ba ne, domin kuwa wadannan sarakuna 'yan aike ne da ke karbar umarni kawai, kuma ba su isa su saba wa yahudawan da suka basu wannan umarni ba.

Bay6anin ya ci gaba da cewa ko shakka babu wannan lamari ba wani sabo abu ba ne ga wanda ya san abin da yake faruwa a tsakanin yahudawan sahyuniya da kuma wadsannan sarakunan larabawa, wadanda ba su ji kungiyar ubangijinsu ba balantana ta mutanen da suke mulka.

Tun kafin wannan lokacin dai gwamnatin wahabiyawan Saudiyya wadda ta sayi mafi yawan srakunan yankin tekun fasha ta sha daukar matakai na kokarin ganin an aiwatar da wannan umarni da aka basu, amma sai yanzu hakan ya yiwu.

Daga karshe bayanin ya kirayi sauran kasashen larabawa da za su zama masu yancin siyasa maimakon zama tamkar rakumi da akala, tare da jinjinawa gwamnatocin da suka yi watsi da wannan kuduri musamamn gwamnatocin Lebanon da kuma Iraki.

3480379

captcha