IQNA

Tunawa Da Zagayowar Lokacin Rasuwar Fatima Zahra A Birtaniya

23:02 - March 07, 2016
Lambar Labari: 3480208
Bangaren kasa da kasa, ana shirin gudanar da tarukan tunawa da zagayowar lokacin rasuwar Sayyida Fatima a babbar cibiyar musulunci da ke Landan Birtaniya.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ic-el.com cewa, wannan shiri za a fara shi ne daga ranar Asabar, kuma za a kwashe darare uku a jere a ana gudanar da shi.

Hojjatol Islam Muhammad Munib da kuma mai wakokin bege Haj Behzad Maulayei ne za su gabatar da jawabi a gaban taron a ranar farko.

Lokacin fara gudanar da wadanna trauka na tunawa da rasuwar Fatima Zahra acibiyar muslunci da ke birnin Landan shi ne daga karfe takwas na dare.

Cibiyar muslunci ta kasar Birtaniya ta gabatar da ta’aziyya dangane da shahadar sayyidah Zahra (SA) ga dukkanin al;ummomin musulmi na duniya, musamman ma mabiya tafarkin Ahlul bait (AS) na duniya baki daya.

3481535

captcha