
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga bangaren yada labarai na cibiyar yada al’adun muslunci na Iran cewa, Sayyid hassan Esmati karamin jakadan kasar Irana akasar Senegal ya gana da Sheikh Ahmad Tijjani Byas babban malamin darikar Tijjaniya a kasar Senegal a garin Gauwlak mai tarazar kilo mita 200 daga Dakar.
Bayanin ya ci gaba da cewa a yayin ganawar tasu bangarorin biyu sun cimma matsaya kan aikewa da makaranta kur’ani mai tsarki daga wannan babbar cibiya zuwa kasar Iran domin halartar gasar kur’ani ta duniya a Iran da za a gudanar.
Mabiya darikar Tijjaniya dai mutane ne ad aka san su da himma matuka wajen gudanar da ayyuka na addini da tsarkake ruhi da kuma son Ahlul bait (AS) kamar yadda lamarin yake a makaranta mazhbar iyalan gidan manzo.
Tun kafin wannan lokacin dawakilin jami’ar Almustafa (SAW) a kasar ya bayyana cewa, akwai dalibai da dama daga bangaren darikar Tijjaniya da ske shirye domin zuwa kasar Iran da nufin karo karatu musamman a bangaren ilmomin kur’ani mai girma.
An gudanar da addu’aoi a ga daya daga cikin manyan darikar Tijjaniya na kasar Muhammad Nyas wanda karamin jakadan Iran tare da babban shehin darikar an akasar Senegal suka gudanar tare.
Kasar Senegal dai ta yi suna wajen bin tafarkin sufanci na darikar Tijjaniya, kamar yadda kuma akan raya taruka na tunawa da iylan gidan manzo kamar Sayyid Zahra (SA) da iyalan gidan manzo a yankunan da mabiya wannan darika suke.