IQNA

An Yabi Babban Mai Daurewa Ta’addanci Gindi A Duniya A taron Masar

16:49 - March 08, 2016
Lambar Labari: 3480211
Bangaren kasa da kasa, taron yaki da ayyukan ta’addanci da aka gudanar a kasar masar ya yabi sarkin Saudiyyah baban mai daukar nauyin ayyukan ta’addanci a duniya a matsayin mai yaki da ta’addanci.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Arab News cewa, taron da ake gudanarwa a Masar a jami’ar syut ya yabi sarkin Saudiyya Salan bin Abdulaziz a matsayin babban mai yaki da kungiyoyin ‘yan ta’adda na duniya.

Taron ya ce sarki yana yin namijin kokari wajen ganin an kawo karshen yan ta’addan takfiriyya da ska addabi al’ummomin duniya.

An gudanar da irin wannan trao na karawa juna sani kan yaki da ta’addanci a shekarar da ta gabata a birnin Makka, domin nunawa duniya sabanin abin da yake faruwa.

Manufar taron dai kamar ydda aka bayyana ita ce kawo karshen hanyoyin da kungiyoyin ‘yan ta’adda suke samun kudade, wannan taro bai yi tsokaci kan manyan masu taimaka yan ta’adda na aduniya, maimakon haka ma ya yabe su ne a matsayin masu yaki da ta’addanci.

3481296

captcha