
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Daily Sabah cewa, tun a jiya ne aka fara gudanar da wannan babban baje koki tare da halartar shugaban cibiyar musulunci ta kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa a wanannwuri ajiye kwafin kur’ani mai tsarki da suka kai guda 150 gami da wasu rubuce-rubuce na musulnci wadanda suke da alaka da tarihin addini.
Wasu daga cikin kwafin kur’anin da ke wurin suna komawa ne tun daga tarihin farko-farko na addini muslunci alokacin halifofin da aka yi bayan ma’aiki.
Bababr manufar gudanar da wannan baje koli dai ita karfafa mutane masu karatu da bincike kan kayan tarihin addinin muslunci dadaddu, da kuma sanin tarihinsu da lokutan da suke komawa zuwa gare su a baya.