IQNA

Rahoton Daily Mail Kan Masallatan Tarihi A Kasar Iran

23:35 - March 10, 2016
1
Lambar Labari: 3480219
Bangaren kasa da kasa, jaridar kasar Birtaniya Daily Mail ta bayar da rahoto dangane da masallata masu tsohon tarihi a Iran wadanda Mehradad Rasuli Fard ya shirya hotunansu.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na veto cewa, jaridar Daily Mail ta kasar Birtaniya ta buga hotunan masallatai na tarihi a kasar Iran wanda Rasuli Fard ya dauka.

Mehradad Rasuli Fard dai wani mai daukar hoto ne dan kasar Iran wanda yak ware, kuma ya dauki hotnan masallatan wadanda aka guina su a kasar tsawon lokuta da ska gabata da fasaha mai ban sha’awa da burgewa.

Kamar yadda kuma ya gudanar da irin wannan aiki a bangarori da daman a bangaren daukar hotuna na dabi’a wadanda suke da tasiri matuka ga masu kallo, wadanda kuma ake buga su a mujallu da jaridu an duniya.

Daga cikin muhimman hotunan da aka buga a wannan jarida wadanda ya dauka,a kawai babban masalalci juma’a na birnin Isfahan wanda ya kai shekaru 900 da ginawa, kamar yadda kuma ya dauki hotunan wasu muhimman wurare na tarihi a wannan birni, da suka hada da hoton masallacin Lotfullh, wanda shi ma ya kai shekaru 400 da ginawa.

Mehradad Rasuli Fard ya saka wadannan hotuna a cikin bangaren hotunan na Istegram, inda ya samu masu sa hannu da ya burge su da ya kai dubu 14.

Wannan mutum ya zama daya daga cikin mutanen da ake buga misali da su ta wanann fuska, domin kuwa babbar manufarsa it ace yada al’adun muslunci da tarihinsa ga sauran al’ummomin duniya.

3482093

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
gaddafi awwal
0
0
our allah believe with us,and forgives our all sin, ameen
captcha