IQNA

Taron Kaddamar Littafi Kan Huzaifa Bin Yaman A Mada’in Iraki

22:41 - March 11, 2016
Lambar Labari: 3480220
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da taron kaddamar da littafi da ya kunshi rayuwar fitaccen sahabin manzon Allah Huzaifah Bin Yaman wanda ya kasance cikin musulmi na farko.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an gudanar da taron mai taken Salman mahadar adinai a birnin Mada’in na kasar Iraki tare da himmar majalisar mabiya mazhabar shi’a na kasar ta Iraki.

An gabatar da kasidu daga jami’on Isfahan, Mashshad,Tunisia, Iraki da sauransu kan matsayin sahabi salman farisi wanda asalin taron kansa ne dake yi karo na sha shida.

An saba gudanar da wannan taro wanda ke da taken salman mahadar addinai, inda bayan gabatar da jawabai da makaloli kan rayuwarsa da kuma gudunmawar da ya bayar domin ci gaban addini, akan dauka daya daga cikin sahabbai a gabatar da makaloli a kansa.

Kamar yadda aka saba a wanan karon an gudanar da kaddamar da wani littafi ne da ya kunshi rayuwar fitaccen sahabin manzon Allah Huzaifah Bin Yaman (RA) wanda ya kasance cikin musulmi na farko, kamar yadda kuma ya ruwaito hadisai masu tarin yawa daga manzon (SAW) da kuma Ahlul bait (AS)

Taron wanda majalisar malaman mazhabar shi'a suka shirya a jami'ar Mada'in da ke Iraki, ya samu halartar wakilan majalisar malaman 'yan sunna da kuma malamai na darikun sufaye a kasar.

Huzaifah ya kasance a sahun gaba wajen yin biyayya ga Imam Ali (AS) bayan manzon Allah (SAW), domin kwa yana biyayya ne gare shi yana mai masaniya kan matsayinsa da hakkinsa a bayan manzo.

3482520

captcha