IQNA

Ganawar Jagora Da Mambobin Majalisar Kwararru

Jama’a Sun Baiwa Maras Da Kunya A Zabe / Aiki Da Manufofin Juyi A Majalisar Kwararru

16:57 - March 12, 2016
Lambar Labari: 3480223
Bangaren siyasa, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei a lokacin da yake ganawa da mambobin majalisar kwarru ya bayyana cewa mutane sun baiwa maras da kunya a zabe, kuma abbab aikin majalisar kwararru shi ne kare manufofin juyin Islama.

Kamfanin dilalncin labaran iqn aya nakalto daga shafin jagora cewa, a safiyar Alhamis ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da shugaba da kuma membobin majalisar kwararru ta jagoranci ta Iran, inda a jawabi mai muhimmancin gaske da yayi, ya jinjinawa al'ummar Iran saboda gagarumar fitowar da suka yi yayin zaben ‘yan majalisun kasar biyu da aka gudanar a ranar 26 ga watan Fabrairun da ya gabata inda ya bayyana hakan a matsayin ci gaba da rikonsu ga tsarin Musulunci da ke gudana a kasar ta Iran.

A jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musuluncin, yayi karin haske dangane da wasu siffofi da wannan zabe ya ke da su, manyan ayyukan da suke gaban ‘yan majalisar kwararru da kuma na majalisar shawarar Musulunci da aka zaba a yayin zaben da kuma bayyana wasu ayyuka guda uku da ya zama wajibi a ba su muhimmanci a kasar Iran bugu da kari kan kokarin da makiya suke yi na kutsowo da kuma yin tasiri cikin gidan Iran, inda ya ce: Hanya guda ta cimma ci gaba na hakika ita ce karfafa tsarin cikin gida a fagaren tattalin arziki, al'adu da siyasa, kiyaye siffofi da koyarwa na juyin juya hali, yunkuri irin na jihadi, kiyaye mutumci da daukaka ta kasa da kuma nesantar narkewa cikin yanayi na kasa da kasa mai hatsarin gaske.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana zaben 26 ga watan Fabrairu da aka gudanar a matsayin wani zabe mai muhimmanci da ma'ana bisa la'akari da fitowar kimanin mutane miliyan 34 da kuma kada kimanin kuri'u miliyan saba'in a cikin akwatuna inda ya ce: A hakikanin gaskiya a yayin wannan zaben mutane sun bayyanar da kansu don kuwa fitowar kasha 62 cikin dari na mutanen da suka cancanci kada kuri'arsu wani kaso ne mai girma idan aka kwatanta shi da na mafi yawa daga cikin kasashen duniya, hatta ma a Amurka.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Ta hanyar wannan gagarumar fitowa, a hakikanin gaskiya mutane sun bayyanar da irin dogaro da kuma yardar da suke da ita ne ga tsarin Musulunci a aikace.

Jagoran ya bayyana zabe ko rashin zaben wasu mutane a yayin zabe a matsayin wani lamari da aka saba da shi, sannan kuma yayin da yake mika godiyarsa ga ‘yan majalisar kwararrun da ba a sake zabansu a yayin zaben ba, Jagoran ya bayyana cewar: Koda yake akwai wasu manyan mutane wadanda zabe ko rashin zabensu koda wasa ba zai haifar da wani gibi cikin rayuwa da kuma mutumcinsu ba, wanda malamai (Muhammad) Yazdi da Misbah suna daga cikin wadannan mutanen wadanda kasantuwarsu a majalisar kwararrun wani lamari ne da zai kara wa majalisar karfi, rashin su kuwa babbar hasara ce ga majalisar kwararrun.

Daga nan kuma sai Jagoran yayi karin bayani dangane da wasu siffofi na musamman na zabubbuka a tsarin Musulunci na Iran musamman ma dai zaben ranar 26 ga watan Fabrairun inda ya ce: ‘yancin da mutane suke da shi na fitowa yayin zaben daya ne daga cikin irin wadannan siffofin, don kuwa a gwamnatin Musuluncin babu tilasci cikin fitowa yayin zaben. Mutane bisa radin kansu da kuma tunaninsu suke fitowa yayin dukkanin zabubbukan da ake gudanarwa.

Ayatullah Khamenei ya bayyana yin takara da gasa a tsakanin ‘yan takara a gwamnatin Musulunci a matsayin siffa ta biyu inda ya ce: Zaben 26 ga watan Fabrairu wani zabe ne da ke cike da gasa tsakanin ‘yan takara da dukkanin ma'anar Kalmar. Don kuwa jam'iyyu da mutane daban-daban ne suka shiga zaben karkashin take da mabambanta, kamar yadda hukumar gidan radiyo da talabijin kuma ta bude fagen yakin neman zabe ga ‘yan takaran majalisar kwararru. A gaskiya dai kowa yayi iyakacin kokarinsa wajen bayyanar da kansa da kuma yakin neman zabe.

Jagoran yabayyana ‘tabbatar da tsaro da kwanciyar hankalin mutane yayin zaben' a matsayin daya daga cikin bangarori masu muhimmanci na zaben inda ya ce: A daidai lokacin da a kasashen da ke makwabtaka da mu mutane suke rayuwa cikin rashin tsaro da hare-haren ta'addanci, to amma an gudanar da irin wannan zabe mai girma da kuma irin wannan fitowa na mutane a kasarmu ba tae da wani hatsari da wani hari mai sosa rai ba, ta yadda a birnin Tehran tun daga karshe 8 na safiya har zuwa tsakar dare suna ci gaba da kada kuri'arsu cikin tsaro da kwanciyar hankali.

Haka nan kuma yayin da yake mika godiyarsa sakamakon kokari da aikin da rundunar ‘yan sanda, jami'an tsaron farin kaya, ma'aikatar cikin gida, dakarun kare juyi da dakarun sa kai na Basij suka yi wajen tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali yayin wannan zaben, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana inganci da kuma kiyayye amana a matsayin daya daga cikin siffofin da wannan zaben ya kebanta da su, daga nan sai ya ce: Sabanin farfagandar makiya da kuma maganganun wasu na cikin gida, a koda yaushe zabe a tsarin gwamnatin Musulunci ta Iran ya kasance mai cike da inganci. Babu wani lokacin da aka taba yin wani yunkuri a hukumance wajen murguda sakamakon zabe.

Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Zaben 26 ga watan Fabrairun nan har ila yau ya sake bayyanar da rashin ingancin maganganu da ikirarin tafka magudin zabe da wasu suka yi a shekarar 1388 (2009) lamarin da ya haifar da wannan fitina mai cutarwa ga kasar nan.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Kamar yadda zaben baya-bayan nan ya zamanto ingantacce ba tare da magudi ba, haka nan zabubbukan da aka gudanar a baya ciki kuwa har da wadanda aka gudanar a 2009 da kuma 2005 suka zamanto ingantattu ba tare da magudi ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana halayyar dattakon da mutanen da suka fadi a zaben suka nuna a matsayin wata siffar ta daban da wannan zaben ya kebanta da shi inda ya ce: Sabanin halayyar rashin dattako da wasu mutanen da suka fadi a zaben 2009 suka nuna da kuma fitinar da suka haifar da ta cutar da kasar nan da kuma karfafa wa makiya gwiwa, a wannan zaben mutanen da suka fadi sun taya wadanda suka yi nasara murna, wanda hakan ba karamin lamari mai girma da daukaka ba ne.

A yayin da yake karkare magana kan wannan bangare na jawabin nasa, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Abin da zaben 26 ga watan Fabrairun yake nunawa shi ne riko da kuma yardar da mutane suka yi da tsarin Musulunci sabanin kokarin da makiya suka yi wajen haifar da ‘karo da juna tsakanin mutane da tsarin Musulunci' da kuma nuna rashin ingancin zaben.

A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da kokarin bata sunan majalisar kula da kundin tsarin mulki (wacce take da alkalin sanya ido kan zaben da kuma tantance ‘yan takara) da makiya suka yi da kuma yin kakkausar suka ga mutanen da suka fada tarkon makiya wajen sanya majalisar kula da kundin tsarin mulkin a gaba yana mai cewa: Majalisar kare kundin tsarin mulki dai ta gudanar da aikinta da dukkan karfinta. Idan ma har akwai matsala, to hakan yana da alaka ne da doka, wanda sai a gyara.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Binciken dacewar ‘yan takara dubu 12 cikin kwanaki ashirin wata matsala ce ta doka wadda wajibi ne a magance ta. To amma bai kamata saboda wannan matsalar a sanya majalisar kula da kundin tsarin mulkin a gaba da suka ba.

Haka nan kuma yayin da yake magana kan tantance ‘yan takarar zaben, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Shin ba tare da cika sharudda ba, za a iya amincewa da dacewa da kuma cancantar dan takara, sannan shin za a iya ba da amsar hakan a gaban Allah Madaukakin Sarki?

Jagoran ya ci gaba da cewa: A lokacin da majalisar kula da kundin tsarin mulki ta gagara gano sharuddan da aka kafa wajen tabbatar da dacewar dan takara a tattare da wannan takarar, ba za ta iya tantance shi da sanar da dacewarsa ba. Wannan kuwa ba matsala ba ce, face dai aiki ne da doka.

Haka nan kuma yayin da yake bayyana cewar majalisar kula da kundin tsarin mulki daya ne daga cikin cibiyoyi na asali na tsarin Jamhuriyar Musulunci a Iran wadda tun farko-farkon nasarar juyin juya halin Musulunci ma'abota girman kan duniya suke ta yada farfaganda da shafa mata kashin kaji, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Duk wani kokarin bata sunan majalisar kula da kundin tsarin mulki, wani aiki ne da ya saba wa Musulunci, ya saba wa doka, ya saba wa shari'a sannan kuma ya saba wa koyarwar juyin juya hali.

Jagoran ya ci gaba da cewa: A dabi'ance mutanen da ba a tantance su ba za su yi fushi, to amma bai kamata su bata sunan majalisar kula da kundin tsarin mulkin ba. Face dai suna iya amfani da hanyoyin doka wajen nuna fushi da rashin amincewarsu.

Bayan bayanin siffofi da kuma sakonnin da suke cikin zaben 26 ga watan Fabrairun, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyaan cewar: Mutane dai sun sauke nauyin da ke wuyansa ta hanyar fitowar da sukayi. Don haka yanzu dai ya rage wa jami'an gwamnati su sauke na su nauyin.

Jagoran juyin juya halin Musuluncin dai ya fara ne da bayanin nauyi da ayyukan ‘yan majalisar kwararru ta jagoranci da aka zaba a matsayin majalisar na daya daga cikin cibiyoyi masu muhimmanci na tsarin Jamhuriyar Musulunci na Iran inda ya ce: aikin majalisar kwararrun dai su ne: "ci gaba da zama mai riko da tafarkin juyin juya hali, tunani irin na juyin da kuma aiki irin na juyin juya hali".

Jagoran ya bayyana kiyaye wadannan siffofi guda uku a yayin zaben jagoran juyin juya halin Musulunci a nan gaba a matsayin a matsayin mafi girman nauyi da aikin da ke wuyan majalisar kwararrun inda ya ce: Wajibi ne a yi watsi da bangaranci da maslaha ta kashin kai ko bangaranci yayin zaben jagoran juyin juya halin Musulunci a nan gaba. Kawai Allah da kuma bukatun kasa da kuma gaskiya ne za a sa a gaba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: Matukar dai aka yi kasa a gwiwa yayin sauke wannan gagarumin aiki, ko shakka babu za a fuskanci matsala cikin aiwatar da aiki gwamnatin da kuma kasa.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da kasantuwar malama da manyan mutane a wannan majalisar ta kwararru, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana yin bayanin matsaloli da bukatun mutane ga jami'an gwamnati da kuma bayyana wa mutane hakikanin yanayin da ake ciki a matsayin daya daga cikin nauyin da ke wuyan majalisar.

Dangane da nauyin da ke wuyan sabuwar majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran din da aka zaba kuwa, Jagoran ya sake maimaita kiran da yake musu ne wajen hadai kai da kuma taimakon gwamnati don cimma manufofinta inda ya ce: koda yake wannan hadin kai da kuma taimakawa gwamnatin, ba wai yana nufin majalisar ta rufe ido dangane da ayyukanta da tsarin mulki ya ayyana mata ba ne.

Daga nan kuma sai Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da ayyuka da kuma nauyin da ke wuyan jami'an gwamnati (bangaren gudanarwa) inda ya ce: A halin da kasar nan take ciki a halin yanzu, wajibi ne jami'an gwamnati su ba da muhimmanci ga wasu abubuwa guda uku, su ne kuwa: 1- Tattalin arzikin gwagwarmaya da dogaro da kai, 2- Ci gaba da bin tafarkin ciyar da ilimi gaba na kasa da aka dauko, sai kuma na 3- Ba da kariya ga al'adu na kasa, al'umma da kuma matasa.

Dangane da batu na farko, Ayatullah Khamenei ya sake jaddada cewa ba za a taba magance matsalar tattalin arziki da ake fuskanta ba tare da aiwatar da siyasar tattalin arziki na dogaro da kai ba, haka nan kuma ba za a sami ci gaban tattalin arzikin ba. Jagoran ya bayyana cewar: An tsaya a kan cewa gwamnati za ta kafa wata cibiya ta bin diddigin siyasar tattalin arziki na dogaro da kai da kuma kafa mai kula da wajen, wanda an yi hakan, to amma wajibi ne a ga aikin hakan a kas a kuma ji shi a jiki.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Wajibi ne jami'an gwamnati sun ayyana da kuma bayyanar da ayyukansu da kuma kokarin da suke yi a bangaren tattalin arziki su yi daidai da wannan siyasa ta dogaro da kai. Wajibi ne ma'aunin kowane shiri na tattalin arziki na gwamnati ya zamanto shi ne wannan siyasar tattalin arzikin na dogaro da kai wanda aka tsara shi bisa tunani da hikima da kuma kwarewa wanda mafi yawa daga cikin masana tattalin arziki sun yi na'am da shi.

Yayin da yake Magana kan batu na biyu kuma, wato ci gaba da riko da tafarkin ci gabantar da ilimi, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: matukar dai muna son samun karfi, daukaka da kuma fadi a ji a duniya, to wajibi ne mu karfafa ilimi. Kada mu dakatar da yunkuri na ilimi.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: wajibi ne a dauki ci gaban ilimi da dukkan karfi, don kuwa daya daga cikin sakamakon hakan shi ne samar da karfafaffen tattalin arziki.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da abu na uku mai muhimmanci da ya kamata jami'an gwamnatin su ba shi muhimmanci wato "kiyaye al'adu' na kasa, Ayatullah Khamenei cewa yayi: Don kiyaye al'adu na kasa, wajibi ne tun da fari wajibi ne mu yi amanna da kuma yarda da wannan manufar, daga nan sai mu yi tsare-tsare da kuma kokari wajen cimma wannan manufar.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Matukar dai jami'an gwamnati suka ba wa wadannan batutuwa muhimmanci, to sakamakon hakan shi ne samun ci gaba na hakika a kasar nan.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana ci gaba na boge ta hanyar ci gaba na zahiri da shigo da kaya daga waje don faranta ran mutane na wani lokaci a matsayin wani lamari mai cutarwa ga al'umma, daga nan sai ya ce: Wajibi ne a samar da ci gaba na hakika wanda ya ginu bisa abin da ake samarwa a cikin gida.

Jagoran ya bayyana "kiyaye siffofi na juyin juya hali, yunkuri irin na jihadi, kiyaye daukaka da mutumci na kasa da Musulunci, nesantar narkewa cikin al'adu, tattalin arziki da siyasa na kasa da kasa masu hatsarin gaske" a matsayin daya daga cikin abubuwan da ake bukata wajen tabbatar da ci gaba na hakika. Har ila yau kuma yayin da yake ishara da tsare-tsaren makiya na kokarin kutsawa da yin tasiri cikin gidan Iran, Jagoran ya bayyana cewar: Bisa ingantattun bayanai, babban aikin da ma'abota girman kai da kuma Amurka suka sa a gaba shi ne neman kutsawa cikin kasar Iran. Koda yake wannan kokarin na su ba wai ta hanyar juyin mulki ba ne, don kuwa sun san cewa a irin tsari na Jamhuriyar Musulunci hakan ba lamari ne mai yiyuwa ba. A saboda haka suna son cimma wannan manufa ta su ta son yin tasiri cikin Iran ta hanyoyin biyu.

Jagoran ya bayyana kokarin yin tasiri a kan mutane da jami'an gwamnati a matsayin manyan manufofi guda biyu da makiya suke son cimmawa ta hanyar kutsawar da suke son yi a Iran, don haka sai ya ce: manufar makiya wajen yin tasiri a kan jami'an gwamnati ita ce sauya irin mahanga da matakan da jami'an gwamnatin suke dauka, wanda sakamakon hakan shi ne fadawa tarkon makiyan da yin abubuwan da suke so. A saboda haka babu bukatar su shigo da kansu kai tsaye, ta yadda shi wannan jami'in gwamnatin ba tare da ya sani ba zai dinga daukar matakan da makiyan suke so.

Jagoran ya bayyana cewa daya abin da makiyan suke so shi ne yin tasiri cikin imanin mutane dangane da Musulunci, juyin juya halin Musulunci, siyasar Musulunci da irin ayyukan na kasa da ya hau kansu, don haka sai ya ce: Kore ‘yancin kai na kasa ma yana daga cikin bangarorin da makiya suke son samun kutsawa, wanda wasu mutane a cikin gida ma suna gabatar da hakan, suna cewa batun ‘yancin kai dai wani tsohon lamari ne wanda a yau dai ba shi da wata ma'ana.

Ayatullah Khamenei ya bayyana kokarin sauya irin Imani na mutane da kuma sanya su mantar da mutane irin ha'incin da kasashen yammaci suka yi wa al'ummar Iran a matsayin daya daga cikin tsare-tsaren makiya inda ya ce: A farfagandarsu suna fadin cewa me ya sa Jamhuriyar Musulunci da jami'anta suke irin wannan adawa da kasashen yammaci da kuma Amurka?

Jagoran ya bayyana cewar: Saboda mu dai mun fuskanci cutarwa ne daga kasashen yammaci, bai kamata mu mance da abubuwan da kasashen yammaci suka yi mana ba. Ni dai ba wai ina goyon bayan yanke alaka da kasashen yammaci ba ne, to amma wajibi ne mu san da wa muke mu'amala?

Har ila yau yayin da yake nuni da bayyanannun misalan irin kiyayyar da kasashen yammaci suke nunawa wa al'ummar Iran tun daga lokacin mulkin Kajariyawa har zuwa yau, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: raunin da sarakunan Kajar shi ne abin da ya share fagen irin matsin lamba da cutarwar kasashen yammaci da kuma dakatar da ci gaban al'ummarmu; daga nan kuma sai Ridha Khan bayansa kuma dansa ya dare karagar mulki; daga nan kuma sai aka kawo karshen yunkurin ‘yan kasanci a ranar 28 ga watan Mordad na shekarar 1332 da kuma samar da ‘yan sandan zaluncin nan na Savak.

Ayatullah Khamenei ya bayyana lalata ayyukan gona, dakatar da ci gaban ilimi, kwadaitar da masana da fitar da su waje bugu da kari kan lalata dabi'un matasa da sanya su shaye-shaye a matsayin wasu daga cikin tsare-tsaren da gwamnatin Shah ta yi karkashin jagorancin Amurka. Daga nan sai ya ce: Tun farko-farkon nasarar juyin juya halin Musulunci kasashen yammaci suka fara nuna kiyayyarsu, suka ci gaba da ba da taimakon kudi da makamai da goyon baya na siyasa ga masu adawa da juyin juya halin Musulunci a kan iyakokin kasar nan. Sun ta yada farfaganda a kan Imam, juyin juya halin Musulunci da kuma jami'an gwamnati, sun nuna kiyayyarsu, haka nan kuma yayin kallafaffen yaki sun yi dukkanin abin da za su iya wajen ba wa Saddam taimako na soji da siyasa da bayanan sirri.

Jagoran ya bayyana dankara nau'oi daban-daban na takunkumi a kan kasar Iran a matsayin wani misalin na daban na irin wannan kiyayyar da suke nuna wa al'ummar Iran, daga nan sai ya ce: Tsarin Jamhuriyar Musulunci dai ba shi da wata niyya ta gaba da kasashen yammaci, face dai su ne suka fara nuna irin wannan kiyayyar sakamakon kafa tushen ‘yancin kai da aka yi a kasar nan.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin yadda kasashen Turai suke bin siyasar Amurka ido rufe cikin lamurra daban daban irin su takunkumin da ta sanya wa Iran da kuma bakar farfagandar da take yadawa kan Iran din, Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa yayi: mu din nan dai muna da nauyin al'umma, kasar nan da kuma tarihinmu a wuyanmu. A saboda haka matukar ba mu yi tsayin daka wajen tinkarar wannan kiyayya ta makiya da dukkan karfinmu ba, to kuwa za su lankwame kasa da kuma al'ummarmu, wanda bai kamata mu ba su irin wannan damar ba.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da maganganun wasu jami'an na cewa wajibi ne mu yi mu'amala da dukkan duniya, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Eh haka ne wajibi ne mu zamanto muna da alaka da dukkan duniya in ban da Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila, to amma wajibi ne mu san cewa kasashen yammaci da Turai ba su ne kawai duniya ba.

Yayin da yake ishara da halartar sama da kasashe 130 suka yi taron kasashen ‘yan ba ruwanmu da aka gudanar a birnin Tehran, Jagoran ya ce: A halin yanzu dai an rarraba karfi duniya zuwa bangarori daban-daban. A yau kasashen gabashin duniya da kuma yankin Asiya ma wasu yankuna ne masu girman gaske.

Har ila yau yayin da yake bayanin cewa tun da fari kasashen yammaci suka fara kiyayya da al'ummar Iran, a halin yanzu kuma suna kokarin neman yin tasiri ne a kasar, Ayatullah Khamenei cewa yayi: Akwai kimanin hanyoyi guda goma da makiya suka tsara wajen yin tasiri a cikin Iran da suka hada da tasiri na ilimi, al'adu da tattalin arziki da kuma neman kulla alaka da jami'oi da masana, halartar tarurruka wadanda a zahiri na kara wa juna sani ne kan ilimi amma da manufar samun yin tasiri a cikin kasa da kuma aikewa da ‘yan leken asirinsu da sunan ayyuka na al'adu.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana karfafa cikin gida a matsayin babbar hanyar fada da wannan kokari na yin tasiri na makiya inda ya ce: Matukar dai kasar Musulunci ta Iran ta tabbatar da karfinta na cikin gida, ko shakka babu wadannan mutanen da a halin yanzu suke ta kokarin nuna girman kai da kada kugen yaki, za su dawo suna shiga layin neman kulla alaka da Iran.

Jagoran ya ci gaba da cewa: A halin yanzu kasashen yammacin suna ci gaba da kai komo, to amma har ya zuwa yanzu dai babu wani abin da wannan kai da komowar ya haifar. Wajibi ne a aikata a ayyana wani irin tasiri da amfani hakan ya haifar. In kuwa ba haka ba, rubuta yarjejeniya a kan takarda kawai ba shi da wani amfani.

Haka nan kuma yayin da yake jinjinawa irin kokarin da jami'an gwamnati suka yi, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Tarihin shekaru 37 na Jamhuriyar Musulunci yana nuni da cewa wajibi ne mu yi karfi a bangarorin tunani, siyasa, tattalin arziki, al'adu da ilimi. A lokacin da muka kai ga wannan matsayin, to kuwa za mu sami daukaka ta hakika.

Tun da fari dai sai da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya jinjina da kuma fatan alheri da rahama ga membobin majalisar kwararru ta jagorancin da suka rasu musamman Ayatullah Wa'iz Tabasi da Ayatullah Khaz'Ali inda ya ce: wadannan ‘yan'uwa guda biyu, a hakikanin gaskiya sun kiyaye matsayin wannan majalisa ta kwararru da kuma gamawa lafiya.

Yayin da yake ishara da tarihin gwagwarmaya na Ayatullah Wa'iz Tabasi da kuma irin hidimar da yayi a lokacin juyin juya halin Musulunci da kuma haramin Imam Ridha (a.s), Jagoran cewa yayi: wannan mutumin, mumuni wanda yake daukar matsayar da ta dace a lokuta masu tsananin muhimmanci, lalle ya tabbatar da matsayinsa na juyi a fili. Sannan kuma a lokacin fitinar shekarar 1388 (2009) yayi watsi da dukkanin abokantaka, ya fito fili ya dau matsayar da ta dace.

Jagoran ya bayyana irin gagarumar fitowar da mutane suka yi a lokacin jana'izar Ayatullah Tabasin a matsayin wani lamari da ke nuni da irin girmama shi da kuma girman matsayin da yake da shi a zuciyar al'ummar Mashhad inda ya ce: Rayuwar wannan babban bawan Allah ba ta sauya ba a lokacin da aka ba shi wannan matsayin da yake kai. Babu wani lokaci da ya nuna wata alama ta jin dadin rayuwa. Ya rasu ne a gidan da yake zaune tun kafin nasarar juyin juya halin Musulunci.

Dangane da Ayatullah Khaz'Ali kuwa, Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa yayi: Shi ma wannan marigayin ya ci jarabawarsa a lokuta masu tsanani. Haka nan haka ya tsaya kyam tare da juyin juya halin Musulunci a lokacin da ake ishara da wasu abubuwan da na kurkusa da shi suka aikata. Wanda haka wani lamari ne da ke nuni da matsayin mutum.

Yayin da yake magana kan yakukuwan da ke faruwa a halin yanzu a yankin Gabas ta tsakiya kuwa, Jagoran ya bayyana cewar yakukuwan sun samo asali ne daga manufofi na siyasa. Jagoran ya ci gaba da cewa: Makiyan Musulunci suna ta kokari wajen mayar da wadannan sabani da ake da su zuwa ga sabani na mazhaba don kada a kawo karshensa cikin sauki. A saboda haka bai kamata su taimaka wa wannan manufa mai hatsarin gaske ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi ishara da kasantuwa da kuma shahadar ‘yan'uwanmu Ahlussunna wajen kare haramin Ahlulbaiti (a.s) da kuma jinjinawa irin wannan matsayi na su yana mai cewa: Bai kamata malamai masu girma su bari Amurka da yahudawan sahyoniya su cimma wannan manufa ta su ta rarraba kan musulmi ba.

Kafin jawabin Jagoran juyin juya halin Musulunci, sai da shugaban majalisar kwararrun Ayatullah Muhammad Yazdi da mataimakinsa Ayatullah Hashemi Shahrudi suka gabatar da jawabinsu da kuma gabatar da rahoto dangane da zaman da majalisar ta gudanar.

3482374

captcha