
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Alkafil cewa, cibiyar Ghadir ta dauki nauyin shirya taro kan Sayyida Zahra (SA) a hubbaren Abbas (AS) tare da hadin gwiwa da masu kula da Hubbaren Imam Hussain (AS) a Karbala.
Bayanin ya ci gaba da cewa taron ya samu halartar darurwan muminai da suka hada da daliban jami’a da kuma hauza gami da wasu daga cikin al’ummar gari gami da sauran malamai masu gabatr da jawabi.
Ustaz Ali Jauhari shi ne ya gabatar da jawabi a wurin, inda ya bayyawa wani bangare daga cikin matsayin da Allah madaukakin sarki ya bata, da kuma irin rayuwarta tare da mahaifinta manzon Allah (SAW) da kuma yadda ta zama babban abin koyi wajen aiki da hakikanin koyarwar manzon Allah.
A wannan taro an karanta tawashi kan irin zaluncin da sayyida Zahra (SA) ta fuskanta a tsawon rayuwarta mai albarka, kama daga lokacin da mahaifinta manzon Allah ya rasu har zuwa lokacin rasuwarta, Sayyid Ahmad Safi na daga cikin wadan suka halrci wannan taro mai albarka.