
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alwafd cewa, cibiyar kula da fatawoyin kafirta muslmi karkarshin babbar cibiyar fatawa ta kasar Masar, ta kirayi kafofin yada labaran turai da su daina yada bayanai marassa tushe kan msulunci da kuma musulmi.
Bayanin ya ci gaba da cewa abubuwa da dama da suke faruwa wadanda kafofin yada labarai na turai ske yadawa kan musulmi da muslunci ba s da tushe balantana makama.
Kamar yadda kuma irin wannan aiki da suke yi ya bayar da dama ga masu tsananin kiyayya da musulunci a ickin kasashe da su ci gaba da yada akidar kyamar musulmi a koina ba tare da la’akari da matsayin msuulmi kana bin da ake danganta musu ba.
Cibiyar ta ce kafofin yada labaran kasashen yammacin turai suna fakewa da abbwan da yan ta’adda irin su daesh suke yi na ta’addanci a matsayin shi ne muslunci kuma shi ne koyawar wannan addini ga musulmi baki.
Alhali abin da ‘yan ta’adda irin su daesh da makantansu suke yi ya fi shafar muslmi fiye da kowane irin mutum mai bin wani addini a duniya, domin kuwa fiye da kasha casein da tara cikin dari na nutanen\n da wadannan yan ta’adda suka kashe kuma suke ci gaba da kashewa muslmi ne.
Wanda hakan ke tabbatar da cewa abin da suke ba muslnci ba ne kuma ba koyarwar wannan addini ba ce, domin kusan kimillar muslmi a duniya bas u yarda da ayyukan ta’addanci da sunan addinin muslunci,kuma sun yi iamnin cewa wannan ba koyarwar addinins ba ce.
A kan wannan cibiya ta kirayi kafofin yada labarai na kasashen turai da su san matsayar musulmi kan kowane irin lamarin kafin yada ko kuma danganta shi da addinin musl;nci ko musulmi,ko da kuwa masu ikirarin addini ska aikata hakan.