
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na World Bulletin cewa, cibiyar musulmi ta IGMG wadda take da rasssa akowane bangare na duniya ta fara gudanar da wani kamfe mai take aminci ni musulmi ne.
An fara gudanar da wannan kamfea yau a kasashen Australia da kuma wasu daga cikin kasashen turai, inda ake gayyatar wadanda ba musulmi ba domin tattanawa da su kan mahangarsu kan addinin muslunci.
Dubban mutane a Australia da wasu kasashen turai suna kokari ta hanyar wannan kamfe domin isar da hakikanin sakon zaman lafiya addininn muslunci.
Bincike dai ya yi nuni da cewa mutanen da bas u da wani addini ko kuma sun yi nisa da addininsu su ne suka fi nuna kyama ga addinin muslunci, kuma musulmi sun fi fuskantar hadari daga gare su.
A birane 6 na kasar Austria an gudanar da irin wannan kamfe, inda musulmi da wadanda ba musulmi ba suka taru suka tattauna tare da juna kuma suka biro da abubuwan da ake samun sabanin fahimta a kansu domin yin bayanai da suka dace kan hakan.
A shekarar da ta gabata an gudanar da irin wannan zama har sau kamar 100 a wasu kasashen trai, inda musulmi kimanin 1000 suka dauki bakunci mutan kikmanin dubu 61 wadanda ba musulmi ba.
A wannan shekara za a gudanar da irin wannan taro sau 150 a wurare daban-daban a cikin kasashen turai.
Masu bukata za su iya neman #HelloIamaMuslim