IQNA

Bayar Da Horo Kan Koyon Karatun Kur’ani A Indonesia

23:41 - March 13, 2016
Lambar Labari: 3480228
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani taro na bayar da horo kan karatu da hardar kur’ani mai tsarki a kasar Indonesia.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin hubbaren Imam Hussain (AS) cewa, babbar cibiyar da ke kula da lamurran kur’ani ta wannan hubbare mai tsarki ce ta dauki nauyi shirya wannan taro na bayar da horo a kasar ta Indonesia a birane da dama da suka hada da Jakarta fadar mulkin kasar.

Muhamamd Bagher Mansuri shi ne wanda ya jagoranci gudanar da wannan shiri a kasar ta Indonesia, ya bayyana cewa shirin ya samu nasara matuka fiye da yadda aka yi tsammani, domin yara 175 ne mata da maza suka shiga shirin, kimanin 30 daga cikinsu sun hardace juzui 29 wasu kuma 30.

Mansuri ya kara da cewa an gudanar da zama 10, inda ake koyar da daliban karatu da harda, kuma shekarunsu sun kama ne daga 4 zuwa 17 babu sama da haka.

3482991

captcha