IQNA

Mata Musulmi A Amurka Sun Fara Koyon Yadda Za Su Kansu

23:33 - March 14, 2016
Lambar Labari: 3480230
Mata Musulmi A Amurka Sun Fara Koyon Yadda Za Su Kansu
Bangaren kas ada kasa, mata musulmi a kasar Amurka sun fara koyon hanyoyiun da za su bi domin kare kansu daga cin zarafi sakamakon kyamar musulmi a kasar.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na CAIR cewa,Ibrahim Huwair shugaban cibiyar kare hakkokin musulmi a Amurka ya bayyana cewa, mata musulmi sun fara daukar matakan kare kai.

Ya ce a cikin yan watannin da suka gabata mutanen da suka fuskanci cin zarafi saboda su musulmi kimanin kasha 80% mata ne.

Huwair ya ce hare-haren ta’addancin da aka kai kwanakin baya acikin jahar California hakan ya sanya kyamar musulmi ta karu matuka acikin garurwan da ke jahar a cikin lokutan nan fiye da lokutan baya.

Ya kara da cewa bayan kai harin 11 ga watan Satumba an samu matsala ta kyamar musulmi inda ake kallonsu a matsayin yan ta’adda a wannan jaha, amma a halin yanzu lamarin ya ninka fiye da kowane lokaci da ya gabata, tare da daukar matakai mafi muni da ake yi kan musulmi.

Wata kungiaya mai kare hakokin musulmi mai suna Buraij ta bayar da bayanin cewa, wata kididdiga da aka samu daga jami’an yan sanda ta nuna cewa, hare-hare kan msuulmi da kuma cin zarafinsu a halin yanzu ya ninka har sau biyar idan aka kwatanta da lokutan baya.

A kan haka ne musulmi suka fara ganin cewa ya zama wajibi su fara daukar matakan koyon kariyar kai daga masu zaluntarsu da nuna musu kyama.

Anji Abdulkadir, mataimakin cibiyar ta Buraij ya bayyana cewa, wannan mataki na kariyar kai ya zama wajibi, domin ta haka ne kawai muslmi za su kare kansu daga masu cutar da su.

3483080

captcha