
Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Eyeopener cewa, daliban jami’ar sun suna gudanar da wannan shiri karkashin wani kamfe mai taken (#MyMuslimness).
Bayanin ya ci gaba da cewa a cikin wannan mako an gudanar shirye-shirye masu tarin yawa a karkashin wannan kamfea cikin wannan jami’a ga sauran mutane masu son sanin hakikanin muslunci.
Daga cikin abubuwan da aka gudanar kuwa har da tattaunawa kan hakikanin koyarwar musulunci a bangarori da daman a rayuwa bisa ga hakikanin koyarwa addinida hadisan manzo (SAW), maimakon dogaro da abin da masu kiyayya da muslunci suka fada.
Babbar manufar gudanar da traon dai ita ce kawar da tunani maras kyau dangane da addinin muslunci sakamakon abubuwan da suke faruwa na ta’addanci da ake danganta su da musulmi da addinin muslunci.
Alhali kuwa shi addinin muslunci addini ne na zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsa da sauran addinai.
Nushaba Fatimashugabar majalisar mata musulmi a wanmnan jami’a ta bayyana cewa, bayan fara gudanar da wannan shiri, dalibai da dama wadanda ba musulmi ba sun yi farin ciki da hakan, kuma suna ta nuna sha’awar sanin mene ne addinin muslunci.
Fatim ta ce a cikin mako guda da aka gudanar da wannan shiri, sun samu gagarumar nasara, ta samun fahimtar juna da kuma kula alaka da bangarori daban-daban na dalibai masu addinai da akidu da suka hada da kiristocin Catholic, kuma an ajiyev a kan cewa za a ci gaba da tattaunawa domin kara samun fahimtar juna.